1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: An zargi 'yan sanda da kisan mutane

Ramatu Garba Baba
November 1, 2017

Wata kungiya ta masu fafutukar kare hakkin bil'adama a Kenya ta zargi 'yan sandan kasar da kisan masu zanga-zanga goma sha uku a tungar 'yan adawa biyo bayan gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2msB3
Kenia Wahlwiederholung Ausschreitungen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/D. Bandic

Kungiyar ta ce 'yan sanda sun yi anfani da karfin da ya wuce kima a rikicin da ya barke a yayin sake zaben shugaban kasar, baya ga haka ta ce ta tattara bayanai ta hanyar anfani da kimiyar zamani don bai wa iyalai ko wadanda lamarin ya shafa sheda don shigar da kara kan cin zarafin da suka fuskanta da ma wadanda suka rasu wani nasu. A watan da ya gabata kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch da ke rajin kare hakkin dan Adam sun ce 'yan sanda a Kenya sun halaka magoya bayan jam'iyyar adawa 67 a rikicin da ya barke bayan da kotun koli ta soke sakamakon zaben farko da ya gudana a watan Agusta.