1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lauyoyin Kenya na kokarin hana a kai 'yan sanda Haiti

May 18, 2024

A Kenya, lauyoyi na kokarin dakile shirin kasar na tura wa da jami'an 'yan sanda zuwa Haiti domin su kwantar da tarzoma, a karar da aka shigar wata kotu.

https://p.dw.com/p/4g1Vn
Lauyoyi a Kenya na yunkurin dakile shirin  tura 'yan sanda zuwa Haiti
Lauyoyi a Kenya na yunkurin dakile shirin tura 'yan sanda zuwa HaitiHoto: Odelyn Joseph/AP Photo/picture alliance

Wannan yunkurin na lauyoyin na zuwa ne kwanaki gabanin jami'an 'yan sandan su isa kasar domin kwantar da tarzoma.

Babbar kotun kasar ta bayar da umurnin cewa a mika bukatar ga manyan jami'an gwamnatin kasar kana ta daga saurar karar zuwa ranar 12 ga watan Juni na shekarar 2024.

Karin bayani: 'Yan Kenya na adawa da matakin gwamnatin na tura 'yan sanda a Haiti

Tun dai a watan Yulin bara ce, kasar Kenyar ta yi tayin tura wa Haiti jami'ai 1,000 domin taimaka wa kasar wajen magance matsalar tabarbarewar tsaron da ta ke fuskanta. Kasashen Jamaica da Bahamas da Benin da Chadi da kuma Bangladesh suma sun yi alkawarin tura wa Haitin jami'an kwantar da tarzoma.