SiyasaIndonesiya
Prabowo Subianto zai dauki madafun ikon Indonesiya
April 24, 2024Talla
A wannan Laraba, hukumar zaben kasar Indonesiya ta tabbatar da Prabowo Subianto a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar, inda zai dauki madafun iko a matsayin shugaba na gaba a kasar ta uku wajen girman tsarin dimukaradiyya a duniya.
Subianto mai shekaru 72 da haihuwa zai karbi ragamar kasar a watan Oktoba, daga hannun Shugaba mai barin gado Joko Widodo wanda yake da farin jini. Shi dai Prabowo Subianto ya samu nasara a zagayen farko inda ya doke sauran 'yan takara biyu, tare da samun fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kuma adadin da ake bukata wajen kauce tafiya zagaye na biyu.