1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun nemi sakin fursunonin siyasa

Suleiman Babayo MAB
April 30, 2024

Manyan 'yan adawa na Tunisiya sun bukaci sakin fursunonin siyasa kafin shiga zaben shugaban kasa da aka tsara cikin wannan shekara ta 2024.

https://p.dw.com/p/4fNAd
Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Kais Saied na Tunisiya
Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Kais Saied na TunisiyaHoto: Hasan Mrad/DeFodi Images/picture alliance

Jiga-jigan 'yan adawa na Tunisiya a wannan Talata sun bayyana cewa za su shiga zaben shugaban kasa cikin wannan shekara ta 2024 idan Shugaba Kais Saied ya saki fursunonin siyasa a kasar tare da dawo da 'yancin bangaren sharia.

Fiye da 'yan adawa 20 suke garkame a gidan fursuna sakamakon matakan da shugaban ya dauka a shekara ta 2021 lokacin da ya karfafa ikonsa a kasar da ke yankin arewacin nahiyar Afirka. Mutane kalilan suka kada kuri'a a zaben raba gardama game da sabon kundin tsarin mulkin. Lokacin shugaban ya dakatar da majalisar dokoki sannan ya rubuta sabon kundin tsarin mulki. 'Yan adawa a kasar ta Tunisiya sun nuna damuwa kan rashin iya samun zaben gaskiya da adalci duba da halin da kasar ta samu kanta.